Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya, NAFDAC, ta ce, ranar Talatar nan za ta soma gwaji kan ingancin taliyar Indomie a fadin kasar.
Ta bayyana haka ne a jiya Litinin sakamakon rahotannin da ke cewa taliyar na dauke da sinadarin ethylene oxide wanda ke haddasa cutar daji.
A wata sanarwa da ta fitar, Shugabar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce: “Sashen da ke kula da ingancin abinci na hukumar tasu zai fara gwaji kan taliyar Indomie a ranar 2 ga watan Mayun nan.
Ta ƙara da cewa abin da ake son dubawa din shi ne sinadarin ethylene oxide. Tuni an bai wa daraktan kula da dakunan gwajin abinci wannan aikin. Yana aiki kan fayyace bayanan da aka tattara,” ta ce.
A wata sanarwa da ta fitar, Shugabar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta ce: “Sashen da ke kula da ingancin abinci na hukumarmu zai fara gwaji kan taliyar Indomie da jayinta a ranar 2 ga watan Mayun nan.
Abin da ake son dubawa din shi ne sinadarin ethylene oxide. Tuni an bai wa daraktan kula da dakunan gwajin abinci wannan aikin. Yana aiki kan fayyace bayanan da aka tattara.