Home » Gwamnatinmu Za Ta Gyara Ma’aikatun Gwamnati – Abba Gida-gida

Gwamnatinmu Za Ta Gyara Ma’aikatun Gwamnati – Abba Gida-gida

by Anas Dansalma
0 comment
Gwamnatinmu Za Ta Gyara Ma'aikatun Gwamnati - Abba Gida-gida

Zababben Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa za ta himmatu wajen gyara ma’aikatun gwamnati a wani yunkuri na karfafa tsarin samar da ayyuka masu inganci.

Abba Kabir, ya bayyana cewa, kamar yadda yake a cikin tsarinsu, za su kafa Cibiyar Horar da Ma’aikatan Gwamnati don dacewa da mafi kyawun ayyuka na duniya

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran Zababben Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanya wa hannu.

Zababben Gwamnan ya taya ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu da ke jihar murnar zagayowar Ranar Ma’aikata ta shekarar 2023.

Ya ce ma’aikata su ne jigon samar da shugabanci na gari a duk wani tsarin dimokuradiyya, don haka sun cancanci a yaba musu bisa sadaukarwar da suke yi wajen gudanar da aikinsu.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya ba wa ma’aikatan jihar tabbacin samun ingantacciyar walwala da ya hada da gaggauta biyan albashi da fansho daga gwamnatin Jam’iyyar NNPP mai jiran gado.

Injiniya Abba ya ce gwamnati mai jiran gado na sane da matsalolin da ma’aikatan jihar ke fuskanta da suka hada da rashin kyawun yanayin aiki da rashin isassun ma’aikata da dai sauran matsaloli wanda kuma ya yi alkawarin gyara su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?