Za mu samu Naira tiriliyan 1 daga noma ~Gwamnan Neja

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya ce gwamnatinsa tana sa ran samun  Naira tiriliyan ɗaya na kudin shiga da za a samu daga Kanfanin Samar da Abinci da Sufuri na Jihar a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Mashawarci na musamman ga gwamnan kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Abdullberqy Ebbo, ne ya bayyana a hakan a ciki wata sanarwa da ya fitar a jiya a Abuja.

A cewarsa, wannan shiri da gwamnati ke yi, zai samar wa da  manoma dubu 100 aikin yi waɗanda ake sa ran za su noma kusan hekta dubu 100 a fadin jihar.

Ya ce tuni aka ƙulla yarjejeniya tsakanin shugaban kanfanin samar da abincin na jihar Neja, Sammy Adigun, da kuma babban daraktan kanfanin TGI, Sadik Kassim.

 

Kuma a ƙarƙashin yarjejeniyar, gwamnatin jihar da kuma kanfanin samar da abincin za su ɗauki alhakin noma, da girbi da sayar da abubuwan da za a noma da suka haɗa da shinkafa da waken suya da masara da riɗi  ga kanfanin na TGI.

 

Kuma za a tabbatar da an samar da sama da tan dubu ɗari shida na kayan amfanin goma a cikin tsawon shekarun biyar masu zuwa.

Post masu alaƙa

Yan sanda sun kama mutane 79 tare da kwato kwayoyi da makamai a bikin Takutaha a Kano.

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da damfarar masu neman aikin gwamnati Naira miliyan 40.

Sabuwar majalisar gudanarwa ta POLAC za ta mayar da hankali kan inganta da ilimi da horo.