Najeriya ta Amuka sun amince da ƙarfafa haɗin kan tsaro tsakaninsu domin yaƙi da ta’addanci.
Cikin wata sanarwa da kakain shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce an cimma hakan ne a ganawar da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu ya yi da mataimakin shugaban Amurka, JD Vance da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio a birnin Washington.
Ganawar na zuwa ne yayin da ake fargabar ƙaruwar ƙaruwar matsalar tsaro a wasu sassan arewa ta tsakiyar ƙasar, lamarin da ya haifar da ƙarin matsin lamba daga gwamnatin Amurka.
A ranar Juma’a sojojin ƙasar suka ce sun kashe mayaƙan ISWAP aƙalla 50 a wani hari da suka yi niyyar kai wa sansaninsu a jihar Yobe.
Gwamnatin Najeriya dai ya musanta cewa ana ƙaddamar da hare-haren ne domin muzguna wa wani addini na daban.
