Hukumar kula da gidajen rediyo da talbijin ta Najeriya (NBC) ta ci tarar gidan talbijin ɗin Channels, naira miliyan biyar saboda saɓa doƙar yaɗa labarai a wata hira da ya yi da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party a zaɓen da ya gabata.
Kamfanin dillancin labarai ta ƙasar, NAN ce ta ruwaito cewa, wannan matakin na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da shugaban hukumar ta, Balarabe Shehu Illelah ya sanya wa hannu, da kuma aka aika wa gidan talbijin ɗin.
Hukumar ta ce ta yi nazarin hirar da Channels ɗin ta yi da Datka Datti Baba-Ahmed ranar Laraba 22 ga watan Maris wanda ta ayyana hirar a matsayin wadda za ta iya tunzura jama’a tare da kawo hargitsi a ƙasar,
Yin hakan, a cewar hukumar ya saɓa wa dokokin yaɗa labaran ƙasar nan.
Don haka hukumar ta sanya wa gidan talbijin ɗin tarar naira miliyan biyar a kan wannan saɓa ƙa’ida, tare da gargaɗin Channels TV da ta kiyaye aukuwar irin hakan a nan gaba.