Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa NDLEA sun cafke wani matashi mai shekaru 34 ɗan asalin Suriname dake ƙasar Amurka mai suna Dadda Lorenzo Harvy Alberto da laifin shigo da ƙullin hodar iblis 117 Nijeriya a da laifin shigo da kullin hodar iblis 117 Nijeriya.
An kama shi ne a filin jirgin sama na Fatakwal dake jihar Ribas.
Kakakin Hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya ce wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya bar kasarsa da ke gabar tekun Arewa maso Gabashin Amurka ta Kudu a ranar 2 ga Afrilu zuwa Sao Paulo da ke Brazil daga kuma Sao Paulo ya sake tasowa zuwa Nijeriya a ranar Juma’a, 7 ga Afrilu, 2023 a jirgin saman Qatar.
Lorenzo ya bayyana cewa, ya shigo Nijeriya ne yana neman mahaifinsa da ya daɗe a Nijeriya wanda yake kira da “Omini.”
A yanzu dai hukumomi sun duƙa wajen gudanar da zuzzurfan bincike a kan wannan al’amari.