• Home  
  • Ndume Ya Koka Kan Sabbin Hare-haren Boko Haram A Borno
- Babban Labari - Labarai

Ndume Ya Koka Kan Sabbin Hare-haren Boko Haram A Borno

Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako. A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da […]

Sanata Mohammed Ali Ndume, ya koka kan yawaitar sabbin hare-haren mayaƙan Boko Haram ƙananan hukumomin Gwoza da Askira/Uba, inda suka kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a ƙarshen mako.

A safiyar ranar Asabar din da ta gabata a garin Ngoshe da ke Gwoza an kashe manoma biyar a lokacin da suke aiki a gonakinsu.

Haka zalika, a yankin Mussa da ke Askira/Uba, wasu ’yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen a ranar asabar da daddare, inda suka kashe matasa uku, kafin su ƙona wasu gidaje da shaguna da ƙauyen.

Waɗannan munanan hare-haren sun jefa al’ummomin cikin zaman makoki wanda ya ƙara nuna damuwa kan rashin kare rayuka da dukiyoyin al’ummar yankin.

Sai dai kuma Sanata Ndume ya yaba da sadaukarwar da sojoji rundunar‘Operation Hadin Kai’ da ke Arewa maso Gabas, bisa nasarorin da aka samu a kan ’yan ta’adda.

Ndume ya bayyana duka abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a matsayin “abin takaici” tare da cewa ci gaba da kai hare-hare a kan al’ummar yankin da ba su ji ba ba su gani ba, musamman manoma da matasa, wani abu ne mai muni na rashin tsaro da ke ci gaba da wanzuwa a Borno ta Kudu.

Sanata Ndume ya tabbatar wa al’ummar Ngoshe, Mussa, da ma ɗauƙacin yankin Borno ta Kudu, kan y\ƙudurinsa na tsayawa tare da su a wannan mawuyacin lokaci.

Ya kuma jaddada cewa, yana aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatocin tarayya da na jihar Borno, da kuma rundunar sojojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro, domin ƙarfafa matakan tsaro a yankunan karkara.

Ya kuma yi qira ga mazauna yankunan da su kasance masu lura da kuma bayar da cikakken haxin kai ga jami’an tsaro domin daƙile hare-haren da za a iya kaiwa nan gaba.

Ya buƙaci a haɗa kai a tsakanin al’ummomi, yana mai jaddada muhimmancinsu wajen tinkarar ƙalubalen ’yan tada ƙayar baya.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai