Jamhuriyar ta sanar da matakin ficewa daga ƙungiyar ƙasashe masu amfani da harshen Faranshi, wato International Organisation of the Francophonie (OIF).
Sanarwar da gwamnatin ƙasar ta tura wa ofisoshin jakadancinta a ƙasanshen duniya a yau Litinin 17 ga watan Maris, wadda ta samu sa hannun babban sakataren gwamnatin ƙasar, Laouali Labo, ta ce “Jamhuriyar Nijar ta yanke shawarar janyewa daga ƙungiyar ƙasashen duniya masu amfani da harshen Faransanci”.
Daga nan sai sanarwar ta buƙaci jakadun ƙasar da su sanar da ƙasashen da suke game da matakin nata.
OIF ƙungiya ce da ta ƙunshi gamayyar ƙasashe 93 daga faɗin duniya, wadda aka kafa domin bunƙasa harshen Faransanci da kuma haɓɓaka cuɗanya tsakanin masu harsuna da al’adu daban-daban.
Sauran manufofin ƙungiyar sun haɗa da haɓɓaka zaman lafiya da ƴancin ɗan’adam, sai kuma bunƙasa tattalin arziƙi da ilimin ƙasashen da ke da wakilci.
Wannan dai na daga cikin matakan da ƙasar ta Jamhuriyar Nijar ke ɗauka na janye jikinta daga ƙungiyoyi da haɗaka na ƙasashen duniya, musamman na yammacin duniya tun bayan juyin mulkin da ya hamɓarar da gwamnatin shugaban ƙasar Mohammed Bazoum.
Ko a baya-bayan nan ƙasar ta Nijar tare da sauran ƙasashe uku masu maƙwaftaka – Mali da Burkin Faso – waɗanda ke ƙarƙashin mulkin soji, sun ɗauki matakin ficewa daga ƙungiyar yammacin ƙasashen Afirka ta Ecowas.