Babban Kwamandan Runduna ta daya ta Sojojin Nijeriya, Manjo-Janar MLD Saraso ya kai ziyarar jaje gidansu wani matashi da ake zargin wani jami’insu da kashewa a Zaria jihar Kaduna.
Ana zargin wani soja da harbe saurayi dan shekara 18, Isma’il Muhammad, a yankin Samaru da ke Zaria jihar Kaduna, a Areacin Najeriya.
Wadan da suka shaida faruwar lamarin sun tabbatar wa manema labarai cewa, an yi harbin ne da karfe 9 na safe a gidan su mamacin da ke layin Sarkin Pawa, yayin da sojojin suke gudanar da sintiri a Unguwar.
- An Kama Ɗan Fashi Da Miliyan 4.9 A Kano
- Kada Ku Yarda Ku Haɗa Kai Da Makiya Dimokuraɗiyya – Shugaba Tinubu
Matashi Isma’il Muhammad na cikin daliban da suka zana jarabawar kammala sakandare a kwanan nan.
Wadan da suka san shi sun tabbatar da cewa yana da burin samun gurbin karatu a makarantar gaba da sakandare, kafin ya gamu da ajalinsa.
Yayin zantawa da mahaifiyar Isma’il, Zainab Sani, ta ce yana wasa ne tare da abokansa da ’yan uwansa a kofar gidan su, sai suka hango motar sojoji ta doso inda suke kuma daya daga cikin sojojin ya nuna su da bindiga, shi ne suka gudu cikin gida.
Sai dai duk da haka sai da sojan da ake zargi ya harbi kofar da Isma’il Muhammad ya dafe ta ciki domin kar sojojin su shigo cikin gidan.
Manjo-Janar Saraso ya ce abin da ya faru a matsayin abin bakin ciki ne, ya bukaci al’ummar yankin su zauna lafiya kuma su kasance masu bin doka da oda