• Home  
  • Yadda Kwankwaso ya sa na yi rantsuwar komawa APC – Abba Kabir
- Babban Labari

Yadda Kwankwaso ya sa na yi rantsuwar komawa APC – Abba Kabir

Kusan kimanin shekara ɗaya bayan komawarsa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya tare da fita daga jam’iyyar NNPP da kuma raba gari da ubangidan siyasarsa Rabi’u Musa Kwankwaso, a karon farko gwamnan Kano Abba Kabir ya yi bayani kan dalilansa na ɗaukar matakin da ya ɗauka. A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar […]

Kusan kimanin shekara ɗaya bayan komawarsa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya tare da fita daga jam’iyyar NNPP da kuma raba gari da ubangidan siyasarsa Rabi’u Musa Kwankwaso, a karon farko gwamnan Kano Abba Kabir ya yi bayani kan dalilansa na ɗaukar matakin da ya ɗauka.

A ranar Litinin 26 ga watan Janairun 2026 gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC a hukumance, bayan sanar da ficewarsa daga NNPP a ranar Juma’a 23 ga watan Janairun 2026, ƙasa da shekara uku bayan cin zaɓen gwamnan Kano a cikinta.

Wasu sun bayyana matakin na Gwamna Yusuf a matsayin ”butulci”, wasu sun ce “cin amana”, yayin da masu ra’ayinsa ke ganin babu ko ɗaya daga cikin waɗannan, kamar yadda shi ma ya faɗa wa BBC.

A tattaunawarsa da BBC Hausa, karon farko tun bayan sauya sheƙa. Abba Kabir Yusuf, ya yi bayanin yadda ya ce ubangidan siyasarsa Rabiu Kwankwaso ya jagoranci yin wata yarjejeniya da shugaban ƙasar Bola Tinubu, domin komawa jam’iyyar APC idan har shugaban ƙasar bai yi katsalanda ba a shari’ar da aka yi kan wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano tsakaninsa da ɗan takarar jam’iyyar APC Nasir Yusuf Gawuna.

Abba ya ce bayan zaɓen 2023 ne suka zauna da shugaban Najeriya, Bola Tinubu, suka yi yarjejeniya cewa idan har bai tsoma baki a shari’ar da ake yi kan neman soke nasarar da ya samu a Kano ba, to za su koma jam’iyyar APC.

Ya ce daga baya Kwankwaso ya yi watsi da yarjejeniyar da suka yi, duk da cewa ya sa shi ya rantse.

“Shi da kansa [Kwankwaso] ya tura ni wajen Tinubu, ya roƙe ni cewa in je in samu Tinubu, in gaya masa mun yi masa wannan alƙawari, kuma ma idan ta kama in ɗauki Alƙur’ani in yi rantsuwa a wannan lokaci cewa idan Allah ya sa mun samu nasara, yana so mu ɗinke gaba ɗaya,” kamar yadda Abba ya shaida wa BBC.

Abba ya ce kuma ya yi hakan, inda ya je wajen Tinubu ya yi masa wannan alƙawari.

Ya kuma ce sau da dama Sanata Kwankwaso ya gana da Shugaba Tinubu, kuma ya sha tura tawaga domin tattauna shirye-shiryen komawa APC.

Abba ya ce duk da cewa Allah ne ya ba shi mulki, a lokacin suna neman fahimtar juna da shugaban ƙasa ne, inda suka roƙe shi kada ya sa baki a shari’ar.

“Kuma an masa alƙawari cewa in Allah ya yarda, idan dai an yi nasara, saboda fahimtar juna da abokantakar da ke tsakaninsa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, an yarda cewa shi Sanata [Kwankwaso] da ni gwamna, a lokacin dukkan magoya baya, in Allah ya yarda, za su koma APC domin a samu haɗin kai,” in ji Gwamna Abba.

A kan haka ne Gwamna Abba ya ce ba ya ji ko kaɗan cewa ya yi wa Kwankwaso butulci, a maimakon haka, ya cika alƙawarin da Sanata Kwankwaso ne ya kasa cikawa.

Waɗannan kalamai na gwamna Yusuf sun dai sha bamban da abin da Sanata Rabiu Kwankwaso ya shaida wa BBC a wata tattaunawa jim kaɗan bayan komawar gwamnan na jihar Kano jam’iyyar APC.

A wancan lokacin Sanata Kwankwaso ya ce fitar gwamna Abba daga jam’iyyar NNPP ta zo da ba-zata ga mutane da dama, kuma shi da kansa jin abin yake kamar a mafarki.

”Da yawa mutane ina da labarin, gani suke ma kamar wani tsari ne, da ni da shi, ko da ni da su. Nima sau da yawa ba na yarda cewar abubuwan da suke faruwa haka su ke,” in ji Kwankwaso.

A tsohuwar tattaunawar Sanata Kwankwaso ya ce ”Ni kaina idan na kwanta sai in waiwaya in ce me ya faru? waye ya yi laifi? Ni ne na yi laifi? jam’iyya ce ta yi laifi? ƴan jam’iyya ne suka yi laifi? amma na kasa samun amsa.”

Sai dai gabanin ficewar da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi zuwa jam’iyyar APC, an ga Sanata Kwankwaso a lokuta da dama yana safa da marwa a fadar shugaban ƙasa, sai dai babu tartibin bayanin da ya bayar a wancan lokacin kan abubuwan da yake tattaunawa da shugaban ƙasar.

Amma duk da haka wasu bayanai dama sun nuna cewa akwai tattaunawar da ake yi ta komawar Kwankwason da gwamna Abba zuwa jam’iyyar APC.

Sai dai a wancan lokacin gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ya ɗauki matakin sauya sheƙar ne bisa la’akari da inda aka dosa a siyasar Najeriya da kuma buƙatar bin hanyar da za ta kawo ci gaba ga jama’ar Kano baki ɗaya.

Ya kuma ce sai da ya yi tuntuɓa a tsakanin abokan tafiyarsa a siyasance da sauran masu ruwa da tsaki kafin yanke hukuncin sauya sheƙar.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai