• Home  
  • PDP Ta Miƙa Wa Kudancin Najeriya Takarar Shugaban Kasa A 2027
- Babban Labari - Labarai

PDP Ta Miƙa Wa Kudancin Najeriya Takarar Shugaban Kasa A 2027

Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027. Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja. A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye […]

Babbar jam’iyyar adawa a Nijeriya, PDP, ta keɓe wa kudancin Nijeriya tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron Kwamitin Zartarwa karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja.

A baya-bayan nan dai wasu masu ruwa da tsaki kan sha’anin siyasa sun zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi wa jam’iyyar takara a Zaɓen 2027.

A yayin taron na yau ne kuma PDP ta tabbatar da Umar Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance.

Damagum wanda ya shafe fiye da shekara guda a matsayin shugaban riƙo na jam’iyyar a yanzu ya zama shugaba mai cikakken iko gabanin babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a gudanar a ranakun 15 a 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na Jihar Oyo.

A watan Maris ɗin 2023, PDP ta naɗa Damagum a matsayin shugaban riƙo, bayan dakatar da shugabanta na wancan lokacin, Sanata Iyorchia Ayu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai