Shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki, ya bayyana shirin jam’iyyar tasu na yin nasara a babban zaɓen 2027.
Turaki na magana ne bayan ganawarsa da tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo a Abeokuta babban birnin jihar Ogun yau Asabar.
Obasanjo ne shugaban ƙasa na farko ƙarƙashin PDP a 1999 kuma ɗaya daga cikin dattijanta a yanzu, yayin da har yanzu take fama da rikicin cikin gida.
Yayin ziyarar, Turaki ya ce yanzu PDP ta fi koyaushe kasancewa cikin shiri “domin dawo da matsayinta a siyasar Najeriya”.
“PDP ta shirya tsaf don tunkarar zaɓen 2027. Amma sai mun fara cin zaɓen Ekiti, da na Osun. Idan muka yi haka babu wanda zai yi tantamar shirin da PDP ta yi na ƙalubalantar rashin iya mulki na APC,” in ji shi.
