Home » Yau Ce Ranar Kula Da Masu Ciwon Sukari Ta Duniya

Yau Ce Ranar Kula Da Masu Ciwon Sukari Ta Duniya

Majalisar dinkin duniya ce ta ware duk Sha-hudu ga watan Nuwambar kowacce shekara, dan yin waiwaye kan halin da masu cutar ciwon sugar suke ciki. domin jan hakali akan cutar da irin hanyoyin kare kai da kuma matakai da masu cutar zasu rika bi don hanata cigaba.

by Zubaidah Abubakar Ahmad
0 comment

Majalisar Dinkin Duniya ce ta ware duk Sha-hudu ga watan Nuwambar kowacce shekara, dan yin waiwaye kan halin da masu cutar ciwon sugar suke ciki. domin jan hakali akan cutar da irin hanyoyin kare kai da kuma matakai da masu cutar zasu rika bi don hanata cigaba.

Cutar suga kan haifar da cutukan koda da zuciya da shanyewar barin jiki, a wasu lokuta ma har ta kan kai ga yanke gabar jiki.

Akan yi maganin cutar ko a jinkirta faruwarta ta hanyar yawan yin gwaji akai-akai.

Ana Wayar da Kan al’umma Kan  Ciwon Suga a duniya kan mayar da hankali kan ƙalubalen da masu cutar ke fuskanta.

Rahotonni sun tabbatar da cewa a Afirka, kusan mutum miliyan 24 ne ke fama da cutar a yanzu. Sai dai abin da ya fi tayar da hankali shi ne, yadda aka yi hasashen adadin zai ninninka cikin sauri. Manyan mutanen da ke ɗauke ciwon suga a Afirka za su ninka, inda za su kai miliyan 57 ko sama da haka in har ba a dauki mataki ba.

Wasu daga cikin alamomin ciwon sugan sun haɗa da:

🚰 Jin ƙishirwa sosai

🚽 Yawan shiga bandaki ko yawan fisari

👁️ Ganin dishi dishi

😴 Jin gajiya

📉 Rama ka rage nauyi ba tare da dalili ba

 

Malam Abubakar yana daya daga cikin masu dauke da ciwon suga. yace masu dauke da wanann cutar sai dai su kara da hakuri domin kamar anragemaka jin dadin rayuwar duniya ne bazakaci zaki ba ba zaka sha mai ko ba, babu tsayayen abinci.

Sannan yayi kira ga mahukuntan lafiya da su taimaka su sasauta harkar magungunar masu ciwon sugan saboda magungunan sun kara kudi sosai ba kamar da ba gashi kuma rayuwa tayi tsada ba kowa ba ne idan likita ya rubuta masa maganin yake iya saya ba.

Ya ce magungunan cutar sun tashi matuka, musamman ma allurai.

Maganin ya fara tashi tun shekara ta 2019. A baya ina sayen magunguna da yawa na ajiye, amma yanzu ba zan iya yin haka ba,” in ji Abubakar

Ya ce a can baya yana sayen maganin (insulin 70-30) kan naira 1200, amma yanzu ya tashi zuwa 12,000.

“Idan kana da kuɗi ba za ka samu matsala ba, in kuma babu za ka ɗanɗana kuɗarka,” in ji shi.

Hanyar da ta fi dacewa don gano ciwon da wuri shine yin gwaje-gwaje na jini da kuma zuwa gani likita don duba lafiyar jiki Lokaci zuwa lokaci.

✅ Kula da nauyin jiki mai kyau

✅ Yin motsa jiki akai-akai

✅ Cin abinci mai kyau

✅ Daina shan taba

Gano cutar da wuri da kuma magani yana da matuƙar muhimmanci don kauce wa matsalolin da ta ke haifarwa ga dan Adam.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?