Real Madrid Na Son Micky Van De Ven, Arsenal Na Iya Sayar Da Jesus

Real Madrid na neman dan wasan baya na Tottenham Micky van de Ven, dan wasan tsakiya na Manchester United Kobbie Mainoo yana son ya tashi a watan Janairu yayin da Arsenal za ta yi tunanin siyar da ‘yan wasanta biyu na gaba.

Real Madrid na sha’awar sayen dan wasan bayan Tottenham Micky van de Ven, mai shekara 24, amma Spurs za su yi tunanin sayar da dan wasan na Netherlands kan fan miliyan 70 kawai. (Fichajes)

Dan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20, na iya neman tashi daga kungiyar don zuwa aro Napoli a watan Janairu idan bai samu karin lokacin wasa a Old Trafford ba. (ESPN)

Arsenal za ta duba batun siyar da dan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 28, da dan wasan gaban Belgium Leandro Trossard, mai shekara 30, a kasuwar musayar ‘yan wasa ta Janairu. (Football Insider)

Post masu alaƙa

Gwamnatin Jigawa ta kashe kusan naira biliyan bakwai (7) domin tallafa wa ma’aikata ta fuskar noma

Jami’an tsaro sun ceto ɗalibai da malaman da aka sace a Kogi

Hukumomin tsaro sun kama wanda ya kirkiri hukumar bogi a Nijeriya