Daga : Shareep Khaleepha Sharifai
Gwamnatin Jihar Osun ta sanya dokar hana fita har na tsawon sao’i 24 a yankin Ifon da Ilobu sakamakon rikicin kabilanci da ya yi kamari a ranar Asabar, inda ya bazu har zuwa ga al’ummar Erin.
Daga nan ne gwamna Ademola Adeleke ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 ga al’ummar da lamarin ya shafa.
Tun farko Adeleke ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 sakamakon rikicin kabilanci da ya raba da matsugunin mazauna Ifon, Ilobu da Erin Osun.
- Cutar Mashaƙo (Diphtheria) Ta Kashe Mutane 1,331 Daga 2022 Zuwa 2025 A Najeriya
- An Kama ‘Yan Daba 12 Kan Zargin Kashe Matashi A Masallaci A Kaduna
An lura da yawa daga cikin wadanda suka rasa matsugunansu a kan titunan Okinni a ranar Asabar, inda wasu musamman ‘yan Arewa suka fito daga yankin a cikin motocin bas.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan Osun, Olawale Rasheed, ya fitar, na daukar matakai na hana afkuwar lamarin, ta ce, “Gwamna Ademola Adeleke ya zage damtse wajen ganin an kawo karshen rikici a rikicin Ifon da Ilobu, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24, da hada rundunar tsaro ta hadin gwiwa tare da daukar nauyin yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin al’ummomin da ke rikici da juna.
“Muna tabbatar wa mutanen Ilobu da Ifon cewa na kuduri aniyar tabbatar da rayukansu da dukiyoyinsu, na sabunta shugabancin ci gaban jihar, muna kan halin da ake ciki.
“A halin da ake ciki, muna neman sanar da jama’a cewa ’yan adawa suna ta yada tsofaffin faifan bidiyo na rikice-rikicen kabilanci a wasu sassan jihar Osun don yada hotunan rashin tsaro na karya a jihar Osun.
Yayin da rigingimun da ke faruwa abin takaici ne, kuma a lokacin da kowa ya tashi tsaye don ganin an kawo karshen tashe tashen hankula, muna sanar da jama’a da su lura da ayyukan ‘yan kasuwan labaran karya da ke tono tsofaffin bidiyoyi don bata sunan gwamnatin jihar. Bidiyon da ake ta yada na tashe-tashen hankula a wasu garuruwa da kauyukan Osun, labaran karya ne, kuma jama’a su yi watsi da su.”