Wasu daga cikin ma’aikatan kafar yaɗa labaran Muryar Amurka (VOA), sun maka shugaba Donald Trump, a gaban Kotu bisa zargin sa da rufe kafar yaɗa labaran ba bisa ƙa’ida ba.
Ma’aikatan sun kai ƙarar ne a kotun tarayya da ke Manhattan ne, inda suka zargi Shugaban Amurka Donald Trump, da babbar mai ba shi shawara, Kari Lake, da take haƙƙinsu ta hanyar rufe kafar babu zato ba tsammani, lamarin da ya saɓa wa dokar ƙasar.
Masu shigar da ƙarar su kimanin shida (6), ciki har da tsohon shugaban ofishin White House na VOA, Patsy Widakuswara, da Editar Press Freedom, Jessica Jerreat, suna neman a mayar da ma’aikatan fiye da 900 da kuma na wucin gadi 550 bakin aikinsu.
- Rikicin kabilanci Ya Sa An Saka Dokar Hana Fita Ta Sa’o’i 24 A Osun
- An Kama ‘Yan Daba 12 Kan Zargin Kashe Matashi A Masallaci A Kaduna
Sai dai da take kare matakin, Kari Lake, ta ce ma’aikatar tana fama da ɓarna da cin hanci, adan haka bai dace kuɗin harajin Amurkawa su ci-gaba da ɗaukar nauyinta ba, kamar yadda kafar yaɗa NPR ta rawaito.
Tunda bayan rufe kafar yaɗa labaran ta VOA, dukkan shafin yanar gizon ta ya kasance ɗauke da tsaffin labarai, baya ga yadda aka daina kama su ta hanyar da ake samun su kai tsare (live streaming).