Home » Mutane 17 sun mutu sakamakon cutar mashako a jihar Kaduna

Mutane 17 sun mutu sakamakon cutar mashako a jihar Kaduna

by Anas Dansalma
0 comment
Mutane 17 sun mutu sakamakon cutar mashako a jihar Kaduna

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar mashaƙo a jihar Kaduna ya kai mutum 17.

An kuma gano mutane 68 da ake zargin sun kamu da cutar a faɗin jihar zuwa ranar Lahadi, kamar yadda gwamnatin jihar ta Kaduna ta tabbatar.

Daga cikin adadin, an samu rahoton mutuwar mutane 14 a Kafanchan da karamar hukumar Jema’a, yayin da uku kuma suka mutu a karamar hukumar Makarfi.

 babban jami’in kula da cututtuka na ma’aikatar lafiya ta jihar, Dokta Jeremiah Daikwo, na cewa ana dakon sakamakon samfuri guda 20 da ma’aikatar ta tattara kuma ta aika domin a yi gwaji.  Mutane 48 da aka kwantar da su kuma na samu kulawar da ta dace.

Dangane da matakin da ma’aikatar ta ɗauka na daƙile yaɗuwar cutar, babban jami’in kula da cututtukan ya ce ma’aikatar ta kara kaimi wajen neman waɗanda suka kamu da cutar da kuma kai su zuwa cibiyar kiwon lafiya domin ba su kulawa

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?