Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta raba Naira miliyan ɗaya ga matasa 36 a shirin haɗin gwiwa na magance aikata laifuka

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ƙara ƙarfafa shirin hana aikata laifuka ta hanyar haɗin gwiwa masu ruwa da tsaki, inda aka bai wa matasa 36 tallafin Naira miliyan ɗaya don su dogara da kansu.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce a baya matasan sun aikata laifuka, kuma yanzu sun daina har suke yin ƙananan sana’o’i don dogaro da kansu , shi yasa aka kirawo su don tallafa mu su.

Tallafin kuɗin wanda, Hon. Baffa Babba Dan Agundi, ya bayar wanda Hon. Nasiru Usman Na’Ibawa, ya wakilce shi, ya jaddada ƙudirinsu na ci gaba da tallafa matasa a koda yaushe.

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya shawarci matasan, su yi amfani da kuɗin yadda ya dace,tare da inganta sana’o’insu.

Shirin bayar da tallafin sana’o’in ya taimaka sosai, na barin aikata laifuka da wasu matasa suka yi, inda suka rike sana’o’insu.

Shugaban majalissar malamai na jihar Kano, Mallam Ibrahim Khalil da masu ruwa da tsaki sun yaba da shirin, tare da yin alƙawarin ci gaba da bayar da goyon baya domin gyaran tarbiyar matasa da wanda zai ƙara tabbatar da tsaron al’umma.

Rundunar ta kuma buƙaci jama’a da masu hannu da shuni da su ci gaba da tallafawa irin wannan shiri domin rage aikata laifuka a cikin al’umma.

Post masu alaƙa

Kotun ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan shari’ar jam’iyyar ADC

Babu wata kotu da ta wanke Murtala Sule Garko daga zargin badaƙalar kudi – Baba Jibo

Kotu ta ba belin mahaifi na – Bello El-Rufai