Rundunar CJTF ta jihar Kano ta ziyarci tashar Muhasa TVR don ƙulla alaƙa a bangare tsaro

Rundunar hadin kan samar da tsaro ta CJTF ta jihar Kano, ta yi kira ga al’umma su mayar da hankali kan tsaron unguwanni da kara sanya ido da irin abubuwan dake faruwa kowanne lokaci, don ci gaba da samun wanzar zaman lafiya mai dorewa.

Kwamandan rundunar CJTF na jihar Kano, Umar Ahmad Baba, ne ya bayyana hakan yayin ziyar zumunchi da kulla alaka da tashoshin Muhasa Telebijin da Radio.

A cewar kwamandan rundunar CJTF na jihar Kano, Umar Ahmad Baba, lokaci ya yi da al’umma za su farka daga baci domin aikin tsaro ba iya na jami’an tsaro ba ne, sai al’umma sun bayar da gudunmawarsu za a samu nasarar da ake da bukata.

Anata bangaren janar manaja ta gidan telebijin da Radio na Muhasa, Hajiya Ai’shatu Sule, ta yaba mu su bisa yadda suka sadaukar da kansu wajen bada tsaro a cikin al’umma, inda ta basu tabbacin basu dama a wasu shirye-shirye don wayar kan jama’a.

A karshe shugabar tashoshin muhasa telebijin da radio, ta ce ya zama wajibi mutane, sauran al’umma su ci gaba da bayar da gudunmawarsu ta kowanne bangare ga jami’an tsaro domin don al’umma suke yin aikin.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *