Rundunar Yan Sanda Ta Musanta Labarin Kai Hari Gidan Wike A Jihar Ribas

 

Rundunar yan sandan jihar Ribas ta musanta rahotannin dake yawo a shafukan sada zumunta, cewar wasu batagarin sun kai hari gidan ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, tare da banka masa wuta.

Tun a ranar Lahadin data gabata rahotannin ke ta yawo a shafukan sada zumuntar cewa an kone gidan kurmus.

Sai dai cikin wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta fitar a ranar litinin, ta ce labarin da ake yadawa bashi da tushe balle makama don haka jama’a su yi watsayi dashi.

Iringe-Koko, ta kara da cewa an yi hakanne don tayar da hankalin al’umma,a saboda haka ba za su lamunci yi wa wasu kage ba don tunzura jama’a ba .

Rundunar ta ce babu wani labari makancin haka da ya faruwa a jihar , inda ta bukaci al’umma da su yi watsi dashi labari ne na kanzon kurege.

Haka zalika rundunar taja kunnen masu yada labaran karya da su daina,domin duk wanda aka samu da aikata laifin rundunar zata daukin matakin shari’a akansa.

A karshe rundunar ta tabbatarwa da mazauna jihar cewa jami’an yan sandan na iya bakin kokarinsu don wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.

Related posts

Tinubu Ya Cire Sunan Maryam Sanda Daga Waɗanda Ya Yi Wa Afuwa

Ba Daidai Ba Ne Tinubu Ya Ci Gaba Da Ciyo Bashi Duk Da Cire Tallafin Mai – Sanusi

Yan Sanda Dubu 45,000 Ne Za Su Kula Da Zaben Jihar Anambra