Siyasa

Kotu ta soke nasarar ɗan takarar ADC a Majalisar Wakilai

Babbar Kotun Tarayya mai lamba biyu da ke Gombe ta soke zaɓen Bashir Abdullahi Gaddafi a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar ADC mai neman kujerar Akko a Majalisar Wakilan Tarayya a zaɓen 2027. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Vera E. Ibrahim, ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ta gudanar da sabon […]

Read more

Tinubu zai fara yaƙin neman zaɓen shi daga Kaduna

Jam’iyyar APC ta sanar da cewa za ta fara gangamin yaƙin neman sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a jihar Kaduna ranar 24 ga Oktoban 2026. A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, ya fitar, jam’iyyar ta ce ƙaddamar da gangamin […]

Read more

Bai kamata ’yan Najeriya suke shan wahala haka ba — Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan tsadar rayuwa da ake fuskanta a Najeriya. A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓensa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku, ya ce gwamnati ta gaza kare ’yan Najeriya daga matsananciyar […]

Read more

Atiku ya naɗa El-Rufai cikin mambobin kwamitin yaƙin zaɓensa

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya amince da kafa kwamitin yakin neman zabensa na shugaban kasa, wanda zai kasance ƙarƙashin jagorancin Kashim Ibrahim-Imam sai Nasir El-Rufai a matsayin mataimakinsa. Naɗin na zuwa ne yayin da El-Rufai ke tsare a hannun hukumomi bisa tuhume-tuhumen da gwamnati ke yi masa. Daraktan yaɗa labarai […]

Read more

Kotu ta soke takarar gwamna da Pantami ke yi a Gombe

Babbar kotun Tarayya da ke zamanta a Gombe ta rushe takarar Farfesa Isa Ali Pantami ɗantakarar gwamnan jihar na jam’iyyar PDP. Kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed, ta yanke hukuncin ne a wata ƙara da Usman Aliyu Garry ya shigar, inda yake ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna […]

Read more

APC ta nada Abdulaziz Yari a matsayin jagoran kamfen na Tinubu

Jam’iyyar APC ta nada tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yakin Neman Zaben Tinubu-Shettima a zaben 2027 da ke tafe.  Da take sanar da kafa Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na 2027 a ranar Asabar, APC ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai kasance shugaban kwamitin, Kashim Shettima a […]

Read more