Home » Rundunar ‘Yan Sanda Ta Shirya Domin Tabbatar da an Yi Zaɓe Cikin Lumana

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Shirya Domin Tabbatar da an Yi Zaɓe Cikin Lumana

by Anas Dansalma
0 comment

A yayin da ake shirin yin zaɓen cike gurbi  a gobe Asabar a rumfuna 2,660 a faɗin ƙasar nan, Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba Alkali ya ba wa masu kaɗa ƙuri’a tabbacin kare lafiyarsu a rumfunan zabe.

Ya kuma ba da umarnin tura ‘yan sanda zuwa kananan hukumomi 185 a faɗin jihohi 24 na tarayyar kasar, inda za a sake gudanar da zabe a ranar Asabar.


Wannan na zuwa ne bayan tashen tashen hankula da aka samu da ya hana masu kada kuri’a zabe a zabukan ranar 25 ga watan Fabrairu da 18 ga watan Maris, musamman a jihohi kamar Lagos da Rivers, da dai sauransu.

A cikin wata sanarwa a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Najeriya, Muyiwa Adejobi, ya ce shugaban ‘yan sandan ya ba da umarnin aikewa da isassun jami’ai da kuma ƙarin kayan aiki don samar da ingantaccen tsaro a zaben da za’a gudanar a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, 2023.


A wani bangare sanarwa ta kara da cewa, “Karin tallafin ya hada da tura ma’aikata, motocin aiki, makamai da rigunan kare kai da kayan kwantar da tarzoma da dai sauransu.


Babban Sufeton ‘yan sandan ya bukaci masu zabe a jihohin da abin ya shafa da su fito sosai domin yin cin gajiyar ‘yancin da doka ta ba su na zaɓe tare da bin doka da oda domin wanzar da zaman lafiya.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?