Home » Rundunar Yan Sandan Kano Ta Fara Binciken Amaryar Da Ake Zargi Da Kashe Mijinta.

Rundunar Yan Sandan Kano Ta Fara Binciken Amaryar Da Ake Zargi Da Kashe Mijinta.

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce, ta fara gudanar da bincike kan wata sabuwar amarya mai suna ,Saudat Jibril, yar shekaru 18, bisa zarginta da kashe mijinta, Salisu Idris , mai shekaru 30, ta hanyar yi masa kisan gilla da wuka.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano , SP Abdullahi Haruna Kiyawa , ta cikin wata sanarwa da ya fitar , ya ce’’ lamarin ya faru a unguwar Farawa, da misalin karfe 12:35am 6 ga watan mayu 2025.

SP Kiyawa ya ce bayan karbar korafin kwamishinan yan sandan jihar, Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, ya tura dakarun yan sanda zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka kai Salisu Idris, asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, wanda likita ya tabbatar da rasuwarsa.

Sanarawa ta kara da cewa , yanzu haka wadda ake zargin tana tsare a sashin gudanar da binciken manyan laifuka don fadada bincike akanta, kafin a gurfanar da ita a gaban kotu da laifin kisan kai.

Kwamishina yan sandan ya ce rundunar yan sandan ba zata lamunci aikata laifuka ba , inda ya tabbatarwa da al’ummar jihar cewa za a yi cikakken bincike don yin adalci ga kowa

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?