Zaɓen 2027: CP Bakori ya gargaɗi jami’an ’yan sanda kan tsoma baki a siyasa.

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya gargaɗi jami’an rundunar da su guji shiga harkokin siyasa, tare da yin aikinsu cikin gaskiya, ƙwarewa da adalci yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2027.

Kwamishinan ya yi wannan gargaɗin ne a wani taron wayar da kan manyan jami’an rundunar kan yadda za a tafiyar da harkokin tsaro a lokacin zaɓe, wanda aka gudanar a wajen shakatawar manyan jami’an yan sanda da ke Bompai a Kano.

Taron ya samu halartar kwamandojin shiyyoyin yan sanda, baturen yan sanda da sauransu.

CP Bakori ya ce aikin ’yan sanda shi ne tabbatar da tsaro da kuma ba kowa damar gudanar da harkokinsa cikin lumana, ba tare da nuna bambanci ga wata jam’iyya ko ɗan takara ba.

Ya kuma yi gargaɗin cewa duk jami’in da aka samu yana shiga harkokin siyasa ko kuma yana yin abin da zai kawo cikas ga sahihancin zaɓe, zai fuskanci matakin ladabtarwa.

Kwamishinan ya bukaci jami’an da su mutunta haƙƙin jama’a da kuma bin doka wajen gudanar da aiyukansu, yana mai cewa hakan ne zai ƙara wa rundunar amincewar al’umma.

Kakakin rundunar yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce rundunar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da jama’a tare da amfani da bayanan sirri wajen tabbatar da tsaro kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen 2027.

Rundunar ta kuma yi kira ga jama’a, jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su guji duk wani abu da zai iya kawo tashin hankali, tare da bin dokokin zaɓe.

Post masu alaƙa

Kamfanin Tianneng ya ƙaddamar da sabbin babura masu kafa biyu da masu kafa uku, waɗanda ke amfani da wutar lantarki, a wani biki da ya gudana a nan Kano.

Kotu ta tsare matasa 11 da ake zargi da kashe dan sanda a Kano

An gano ƙoƙon kai da ƙasusuwan mutum 28 a Abia