Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa yana aiki ba dare ba rana don lalubo mafita kan kalubalen da kasar nan ke fuskanta.
Wannan sako na sallah ya kunshe a cikin wata sanarwa da ya rattaba wa hannu a jiya, inda ya tabbbatar da cewa, gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen sake farfado da tattalin arzikin kasar nan da kuma magance daukacin abubuwan da ke hana kasar ci gaban kasa.
Shugaba Tinubu ya gudanar da sallar Idi ne a Masallacin Idi da ke Obalende daura da barkin soji na Dodan.
Ya ce a yanzu haka Nijeriya na ci gaba da fuskantar kalubale, musamman na tattalin arziki da kuma kalubalen rashin tsaro.
Inda ya tabbatar da cewa yana sane da wadannan kalubalen, kuma yana bai wa ‘yan Nijeriya tabbacin cewa za a shawo kan kalubalen.
Tinubu ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance masu kwarin guiwa don a samar da gobe mai dorewa duk da kalubalen da Nijeriya ke fuskanta.
Ya kuma taya ‘yan kasar murnar babbar Sallah, inda ya yi kira ga ‘yan uwa Musulmi da su yi amfani da sallar wajen taimaka wa marasa karfi.
Ya kuma gode wa Allah SWA bisa damar da ya mu na ganin wannan rana inda ya yi nuni da cewa, hanyar da ya fi dacewa mu nuna farin ciki shi ne mu ci gaba da zama lafiya da kowa da nuna kishin kasarmu.