Home » Sanata Barau I. Jibril ya mika sakon barka da sallah ga ‘yan Najeriya

Sanata Barau I. Jibril ya mika sakon barka da sallah ga ‘yan Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment
Barau Jibril

Mataimakin shugaban majaisar Dattawa Sanata Barau I jibiril ya bukaci musulmin kasar nansu tabbatar da mahimancin bikin sallah ga rayuwra musulmi wajen taimakawa mabukata.

A cikin wata sanarwa daga mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Isma’ila M udasshir ya bukaci musulmi su rika addu’oin nemawa kasar nan zaman lafiya da hadin kai da tsaro da kuma cigban tatalin arziki.

Sanata Barau wanda kuma shine Mataimaki na daya na Shugaban ‘Yan majalisar kasashen dake cikin kungiyar kasashen raya tattalin arziki ta yammacin Afirika ECOWAS ya tabatarwa da ‘yan Najeriya cewa gwamnati mai ci a kasar nan ta dukufa wajen ganin ‘yan Najeriya sun ci moriyar tarun albarkatun kasar nan domin jindadin kowa da kowa.

Mataimakin shugaban majalisar Dattawan, ya kuma bayyana kudirin majalisar na bujiro da dokoki da zasu magance matsalolin dake damun kasar nan bisa bin manufar shugaban kasa ta sabuwar Najeriya.

Da ya juya kan jama’ar kasa, sanata Barau Jibiril ya taya ‘Yan Najeriya murnar babbar Sallah, sannan ya tinatar da musulmin, su inganta imaninsu ga Allah maɗaukakin sarki tare da kiyayewa da umarninsa kamar dai yadda Annabi Ibrahim alaihissallam yayi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi