A yayin da ake cigaba da gudanar da ibadar layya kamar yadda yake a bisa al’ada ta babbar Sallah, rabon naman layya a matsayin sadaƙa a tsakanin al’umma ba sabon abu ba ne idan aka yi la’akari da koyarwa ta addinin Musulunci.
Sai dai wannan sallah ta gamu da yanayi na tsadar kayayyaki da kuma ƙarancin kuɗi a hannun al’umma wanda hakan ya sa abokiyar aikinmu Zubaida Abubakar Ahmad ta kewaya domin jin ko al’umma da dama sun samu zarafin yin layya kuma yaya daɗaɗɗiyar al’adar nan ta rabon naman layya ga maƙota da ‘yan uwa da sauran al’umma mabuƙata take a wannan lokaci, ga kuma abin da ta haɗa mana:
RAHOTO: ZUBAIDA ABUBAKAR AHMAD