Shugaban majalisar Wakilai Abbas Tajuddeen ya hori ‘yan Najeriya su cigaba da yiwa shugabanninsu Addu’oi da fatan alkhairi a kokarinsu na bunkasa cigaban Najeriya ta yadda zata zamanto hamshakiyar kasa.
Ya yi tinatarwar ne a sakona na barka da sallah ga Al’ummar musulmin kasar nan dake bikin Babbar sallah a yau,inda ya jawo hankalin ‘yan Najeriya cewa, sai da sadaukarwa ne kasar nan zata samu cigaban da ake bukata ,ta yadda kowane dan kasa zai gudanar da rayuwa cikin farinciki da kwanciyar hankali.
Shugaban majalisar wakilin Abbas Tajuddeen,cikin sakon nasa mai dauke da sa hannun mai bashi shawara kan harkokn yada labarai,Musa bdullahi Kirishi, yace babban darasin da bikin salla ke koyarwa shine, mika wuya ga Allah Sunhanahu wata’Allah da biyayya ga shugabanni da sadaukarwa.
Don haka ya bukaci ‘yan Najeriya su rika aiki da wadannan dabi’u a harkokin rayuwarsu ta yau da kullum domin dacewa a nan duniya da ranar gobe ƙiyama.
Shugaban majalsa Wakilan Abbas Tajuddeen ya yayiwa musulmin kasar nan barka da sallah da fatan Alah ya karbi ibadunsu ya kuma bukace su,su cigaba da zama lafiy da juna tare da taimakon juna.