Tsohuwar Sanata mace ta farko a Nijeriya, Franca Afegbua, ta rasu tana da Shekaru 81 a Duniya.
An ce ta rasu ne a garin Benin na jihar Edo a wani asibiti mai zaman kansa bayan ta yi fama da rashin lafiya a ‘yan watannin da suka gabata.
Kassim Afegbua, daya daga cikin kannenta kuma dan jarida ne ya tabbatar da rasuwar ta, wanda ya taba rike mukamin kwamishinan yada labarai a gwamnatin Gwamna Adams Oshiomhole a jihar Edo, kuma a halin yanzu mamba ne a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Ya ce ‘yar uwarsa ta rasu ne da safiyar Lahadi, kuma an kai gawarta zuwa dakin ajiyar gawa na jami’ar Benin (UBTH).
Marigayiya Franca Afegbua, an haife ta ne a shekarar 1942 kuma an zabe ta a matsayin Sanata a rusashshiyar jam’iyyar NPN a shekarar 1983, ta wakilci gundumar Bendel ta Arewa a rusasshiyar jihar Bendel. Ta yi aiki a majalisar dokoki daga Oktoba zuwa Disamba 1983 kafin juyin mulkin soja ya kawo karshen Jamhuriyya ta biyu a ranar 31 ga