Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yi Alla-wadai da sace ƙananan yara da ake yi a jihar nan da kuma kai su Kudancin ƙasar nan.
Sarkin ya bayyana rashin jin daɗinsa ne a jiya a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadarsa.
Sarki Kano, wanda Dan Malikin Kano, Ambasada Ahmad Umar, ya wakilta, ya ce masarautar Kano ba za ta lamunci, ci gaba da sace da kuma safarar ƙananan yara ba a jihar nan ba tare da canja musu addini da kuma ƙabila ba.
Ya ce wannan al’amari na ci gaba da ta’azzara kuma wajibi ne a ɗauki mataki na magance wannan matsala.
A cewar mai martaba sarkin Kano, ba za su zuba ido ana sace yara, a sayar da su, sannan a caja musu ƙabila da addini ba.
A ranar 27 ga watan Disambar shekarar da ta gabata ne aka yi nasarar cafke masu safarar mutane, inda aka kama mutane 9 da ke wannan gurɓatacciyar harka a jihohin Kano da Bauchi da Legas da Delta da Anambra da kuma jihar Imo.
Rundunar ‘yan sanda ta kuma ceto wasu yara waɗanda da yawansu ‘yan asalin jiharBauci ne.
Shi ma a yayin da yake jawabi, shugaban ƙabilar Igbo mazauna Kano, Boniface Igbekwe, ya yi Alla-wadai da wannan al’amari tare da kiran mahukunta da su tabbatar da an hukunta waɗanda ake zargi.
Ya ce, al’ummar Igbo mazauna Kano, suna nesanta kansu da waɗanda ake zargin da aikata wannan aika-aika tare da tabbatar da aniyarsu ta ci gaba da rungumar zaman lafiya da al’ummar Kano.
DAILYTRUST AM/HD