Mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira ga Asiwaju Bola Tinubu a matsayinsa na zababbe kuma shugaba mai jiran gado da ya kafa ma’aikata da za ta rika kula da harkokin addini a kasa.
Mai martaba Aminu Ado Bayero ya yi wannan kira ne a tabakin Hakimin Nasarawa, Babba Dan-Agundi wanda ya wakilci Mai martaba Sarki a wajen kaddamar da wani taro na masu aikin hada-kan addinai da ActionAid Nigeria ta shirya a yammacin jiya Juma’a.
Mai martaba Sarkin Kano, ya ce, ya na ganin hakan zai taimaka sosai a wajen kawo hadin-kai da kwanciyar hankali tsakanain Mabiya addinai da ake da su.
Da yake magana, Babba Dan-Agundi ya ce idan an kafa ma’aikatar addinin, za ta maida hankali sosai wajen koyar da hakuri tsakanin mabanbanta addinai.
Haka zalika Hakimin ya ce ma’aikatar za ta bada karfi wajen ganin an samu fahimtar juna.