Home » Sarkin Musulmi ya buƙaci a duba watan Shawwal a Najeriya ranar Asabar

Sarkin Musulmi ya buƙaci a duba watan Shawwal a Najeriya ranar Asabar

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda shi ne shugaban Majalisar ƙoli ta addinin Musulunci a ƙasar ya buƙaci al’umma su duba jinjirin watan Shawwal na shekarar Musulunci ta 1446 (Bayan Hijira) a gobe Asabar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da fadar Sarkin Musulmin ta fitar a yau Juma’a, wadda ta samu sa hannun shugaban kwamitin da ke bai wa sarkin Musulmi shawara kan harkokin addinin Musulunci, Farfesa Sambo Wali Junaidu.

Sanarwar ta ce “Ana sanar da Musulmai cewa Asabar, 29 ga watan Maris, 2025, wadda ta yi daidai da 29 ga watan Ramadan, ita ce ranar da za a yi duban jinjirin watan Shawwal na shekarar 1446 (Bayan Hijira).

“Saboda haka ana buƙatar Musulmai su dubi watan a ranar Asabar, sannan idan sun gani su kai rahoto ga hakimi ko dagacin yankinsu, wanda shi kuma zai isar da saƙon ga Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar.”

Ganin jinjirin watan Shawwal ne zai tabbatar da ƙarshen azumin Ramadan, inda za a gudanar da sallar Eid el-Fitr a ranar ɗaya ga watan na Shawwal.

Idan aka ga jinjirin watan a ranar Asabar, hakan na nufin za a yi hawan sallah ƙarama a ranar Lahadi bayan yin azumi 29, sai dai idan aka gaza ganin watan, Sarkin Musulmin – bisa al’ada – zai bayar da sanarwar cike azumi 30 kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?