Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Muhammadu Sa‘ad Abubakar na uku ya yi kira ga al’ummar Najeriya su cigaba da saka shugabanni cikin addu’oinsu na yau da kullum.
Sultan ya yi wannan kiran ne a jami’ar Illorin a jiya Alhamis a yayin gabatar da lakcar ƙaddamar da wani littafi domin girmamawa ga farfesa Ishaq Oloyede.
Ya ce, ya kamata ƴan Najeriya su daina mummunar al’adar nan ta zagin shugabanni, zaifi kyau su riƙa yi musu addu’a duk da lalacewar su. “Kar ku riƙa zagin shugabannin ku, ko da kuwa gurɓatattu ne su, yi musu addu’ar shiriya shine mafita.” a cewar Sultan.
Ministan Shari’a Na Najeriya Yarima Lateef Fagbemi (SAN) wanda shine shugaban taron, ya yi kira ga ƴan ƙasa da su ɗauƙi ɗabi’ar bawa shugabanni ƙwarin gwiwa domin hakan zai taimaka matuƙa.
“Ba ina cewa ba ma kuskure bane, amma in yan ƙasa suna tofin Allah tsine ga shugabaninsu wannan ba alama ce mai kyau ba.”
“Ina da tabbas a cikin mu akwai masu baƙar zuciya, kuma wannan yana faruwa ko a ƙasashen ƙetare.
“Abin da ya kamata muyi shine mu rage yanda muke caccakar shugabanni” a cewar Lateef Fagbemi.
Sultan Abubakar na ɗaya daga cikin dattawan da yanki m Arewa, kuma mai faɗsa aji ga shugabanni da kuma Mabiya.
Ƴan ƙasa dai na to fa albarkacin bakin su saboda halin ƙunci da suke ciki, inda wasu ke ta’allaƙa matsalolin ga shugabanni.