• Home  
  • Amfanin kokomba a jikin dan Adam
- Babban Labari - Labarai - Lafiya

Amfanin kokomba a jikin dan Adam

Kokomba wani nau’in kayan lambu ne da ke taimakawa wajen saukaka sarrafa abubuwa masu tarin yawa a jikin dan Adam. Masana kiwon lafiya sun ce mutane na cin kokomba ne a matsayin kayan lambu amma tana cikin kayan marmari. Ana amfani da ita a cikin wasu kayayyakin gyaran fata. Kokomba na cikin kayan marmari kamar […]

Kokomba wani nau’in kayan lambu ne da ke taimakawa wajen saukaka sarrafa abubuwa masu tarin yawa a jikin dan Adam.

Masana kiwon lafiya sun ce mutane na cin kokomba ne a matsayin kayan lambu amma tana cikin kayan marmari.

Ana amfani da ita a cikin wasu kayayyakin gyaran fata. Kokomba na cikin kayan marmari kamar kankana, da tupa da dai saauransu.

Kokomba na taimakawa wajen narkar da abinci a cikin ciki.Tana taimakawa wajen rage kiba. Sannan tana taimakawa wajen kara lafiyar kwakwalwa.

Kokomba na warware gajiyar jiki. Sannan tana kunshe da sinadaran vitamin na B1, da B5 da kuma B7. Kokomba na maganin warin baki, da ciwon koda da kuma ciwon ido. Haka kuma tana daidaita karfin bugawar jini daga zuciya, akwai kuma yiwuwar kokoma ta kare mutum daga kamuwa da cutar sankara.

Ina fatan za mu rika ta’ammali da kokomba domin inganta lafiyarmu.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai