Fitaccen Malamin addinin musulunci kuma tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi kira da ya kamata a cire tsarin ba wa shugabanni rigar kariya bayan sun kammala wa’adin Mulki.
Sheikh Pantami ya faɗi hakan ne ya a jiya Lahadi yayin taron shekara shekara da cibiyar Musulmi ta The Muslim Congress (TMC) ta shirya a birnin tarayyar Abuja.
Taken taron dai shine “Gina ingantacciyar ƙasa: Nauyi ne kan shugabanni da mabiya domin tuna ranar Ƴancin Najeriya na 64.
“A addinin musulunci, babu wata rigar kariya da shugabanni suke da ita, wasu lokutan kariyar na da kyau, amma wasu lokutan hakan na jawo matsaloli masu tarin yawa,” a cewar tsohon ministan.
Ya kuma ƙara da cewa bayan mutum ya bar ofis da shekara hudu ko takwas, sai kaga ana ƙalubalantar sa da zarge-zarge masu yawa ma cin hanci da rashawa. Don haka kariyar ba ta hana mutum fuskantar shari’a.
“A shari’ar Musulunci babu wata rigar kariya. Da shugaba da mabiya kowa zai iya fuskantar shari’a, kuma dole ya je ya kare kansa. An yi wa Ali ibn Abi Talib da Umar ibn Khatab suna Khalifanci. Don haka yana da kyau a samar da daidaito a wajen shari’a,” in ji Pantami