Home » Sarkin Yaƙin Masarautar Zazzau Ya Rasu Ana Tsaka Da Taro

Sarkin Yaƙin Masarautar Zazzau Ya Rasu Ana Tsaka Da Taro

by Mubarak Ibrahim Mandawari
0 comment

Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar ɗaya daga cikin manyan fadawan Sarkin Zazzau, kuma Sarkin Yaƙin Zazzau, Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, da safiyar ranar Alhamis yayin da ake tsaka da taro a Babban Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan, Zariya.

Marigayin yana cikin tawagar Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, lokacin da mutuwa ta riske a wajen taron da kwamitin abokai na asibitin ya shirya.

Da yammacin ranar Alhamis, aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Rimin Doko, a Unguwar Kaura, a cikin Birnin Zariya.

Babban Limamin Zazzau, Malam Dalhatu Kasim Imam ne, ya jagoranci sallar jana’izar da aka yi da misalin ƙarfe 5 na yamma.

Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, tsofaffin gwamnonin Jihar Kaduna, Alhaji Ahmad Makarfi da Alhaji Muktar Ramadan Yero, da kuma sauran al’umma ne suka halarci jana’izar.

A saƙon ta’aziyyarsa, Sarkin Zazzau ya jajanta wa iyalan mamacin da ɗaukacin masarautar bisa wannan babban rashi.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?