Sashin lura da al’amuran bashi a Najeriya DMO, ya gargadi gwamnatin tarayya game da ƙarin karbo aron kudi a irin halin da ake ciki.
Inda ya ce, an fadawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama dole ya gujewa cin bashi a yanzu.
Hukumar ba ta goyon bayan cin bashin ganin cewa kashi 73.5 na kudin shigar da za a samu a bana duk zai tafi ne a wajen biyan bashin da aka karbo.
Haka zalika hukumar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta nemi hanyoyin da za tayi wajen ganin ta kara samun kudin shiga a cikin lalitar ƙasar nan.