• Home  
  • Senata Ndume ya buƙaci Tinubu ya janye sunayen jakadu
- Babban Labari - Labarai

Senata Ndume ya buƙaci Tinubu ya janye sunayen jakadu

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye jerin sunayen jakadun da ke gaban majalisar a halin yanzu, bisa zargin cewa an saba wa ƙa’idar tsarin tarayya da kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada. A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne majalisar […]

Ndume

Tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattawan Najeriya, Ali Ndume, ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya janye jerin sunayen jakadun da ke gaban majalisar a halin yanzu, bisa zargin cewa an saba wa ƙa’idar tsarin tarayya da kundin tsarin mulkin 1999 ya tanada.

A ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne majalisar dattawa ta karɓi jerin sunayen waɗanda shugaba Tinubu ke neman ya naɗa, waɗanda aka miƙa wa kwamitin majalisar dattawa kan harkokin ƙasashen waje domin tantance su.

Sai dai Ndume mai wakiltar Borno ta Kudu a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar ya ce jerin sunayen ya ci karo da sashe na 14(3) na kundin tsarin mulkin ƙasar, wnda ya buƙaci a yi daidaito tsakanin ɓangarorin ƙasar wurin bayar da muƙaimai.

Ya ce yayin da wasu jihohin ke da mutum uku ko huɗu, wasu kuma ba su da ko guda ciki har da jihar Gombe.

“A wannan lokaci na rayuwar gwamnatinsa, dole ne shugaba Tinubu ya guji yanke shawarar da za ta iya haifar da rikicin ƙabilanci ko kuma haifar da rashin yarda tsakanin al’umma.

“Ina roƙonsa da ya janye jerin sunayen, ya kuma gabatar da sabbin sunayen waɗanda aka zaɓa wanda zai dace da tsarin mulkin ƙasa,” in ji shi.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai