• Home  
  • NOA Ta Bukaci Masana’antar Fina-finai Ta Inganta Dabi’u Da Martaba Nijeriya.
- Babban Labari - Labarai

NOA Ta Bukaci Masana’antar Fina-finai Ta Inganta Dabi’u Da Martaba Nijeriya.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta bukaci kungiyar masu shirya fina-finai data yi amfani da masana’antar wajen inganta dabi’u da al’adu da martaba Nijeriya. Darktan Janar na hukumar, Mallam Lanre Issa-onilu, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi mambobin kungiyar reshen babban birnin tarayya Abuja. Mallam Lanre, ya ce fina-finai suna […]

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta bukaci kungiyar masu shirya fina-finai data yi amfani da masana’antar wajen inganta dabi’u da al’adu da martaba Nijeriya.

Darktan Janar na hukumar, Mallam Lanre Issa-onilu, ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi mambobin kungiyar reshen babban birnin tarayya Abuja.

Mallam Lanre, ya ce fina-finai suna da tasiri sosai wajen chanja tunani da kuma hada kan kasa , inda ya shaidawa tawagar cewa hukumar NOA na shirin hada kai da masana’antar fina-finan don wayar da kan jama’a cikin shirye-shiryensu na film.

Shugaban masu shirya fina-finai reshen babban birnin tarayya Abuja, Desmond Utomwen, ya yabawa hukumar kan kokarin da take yin a wayar da kan jama’a da inganta dabi’u tare da yin alkawarin hada kai da hukumar don fito da fina-finai da za su wayar da kan yan kasa da suka shafi inganta dabi’u da kishin kasa.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai