Kungiyar Sa-Ido Kan Sarrafa Tattalin Arziki Mai Zaman Kanta (SERAP) ta yi barazanar gurfanar da gwamnatin tarayya a gaban kotu, idan har ta gaza gudanar da bincike kan zargin ɓacewar sama da ganga miliyan 149 na danyen man fetur.
Kungiyar ta fito ƙarara ta yi wa shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, barazana ne a wata wasiƙa mai dauke da kwanan watan 22 ga Afrilu shekarar da muke ciki.
Ta bayyana cewa, tana bukatar gwamnati ta kafa kwamitin bincike na shugaban kasa da zai gaggauta gudanar da bincike kan wannan zargi.
Kungiyar ta kuma bukaci shugaba Buhari da ya tabbatar da hukunta duk wanda ake zargi da hannu wajen wawure dukiyar man ƙasar nan, tare da ƙwato duk dukiyoyin da suka wawure.