Shahararriyar jarumar nan ta masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Rahama MK, wadda aka fi sani da Hajiya Rabi Bawa Mai Kada ta cikin shirin fim mai dogon zango na kwana casa’in ta haifi santaleliyar jaririya a gidan mijinta na gaske.
Jarumar finafinai, Mansura Isah, ce ta bayyana haihuwar a kafar sada zumunta ta Instagram inda take taya Rahama MK murnar samun ƙaruwar ‘ya mace.
Rahama MK ta yi shura a fina finan Hausa musamman shiri mai dogon zango na kwana casa’in wanda a wannan sati ya zo da wani sauyi mai jan hankali bayan lashe zaɓen gwamnan garin Alfawa da ta yi a fim ɗin.