Kamfanin Google ya karrama marigayi dan kwallon Najeriya, Rashidi Yekini ta hanyar sanya zanensa a shafin na google a daidai lokacin da dan wasan ke cika shekaru 60 da haihuwa.
BBC ta rubuta cewa Yekini dai ya faɗa ƙangin talauci da rashin matsuguni bayan yin fice a matsayin ɗaya daga cikin manyan taurarin ƙwallon ƙafa na Najeriya.
Zanen na Google ya kwatanta murnar da Yekini ya yi lokacin da ya ci wa Najeriya ƙwallonta ta farko a gasar cin kofin duniya a 1994.

Hakan ya nuna lokacin da Yekini ya zura ƙwallo a ragar Bulgeriya, ya shige cikin ragar tare da kama ta da hannu bibbiyu yayin da hawayen murna ke kwararo masa.
