Shararriyar mawakiya Onyeka Onwenu ta rasu a daren Talata a jihar Legas bayan ta yi wasa a bikin zagayowar ranar haihuwar wata mata da aka gudanar a Legas.
An tabbatar da mutuwar mawakiyar ne a wani asibiti da ke unguwar Victoria Island a birnin Legas. Sai dai har yanzu dangin Onyeka Onwenu ba su tabbatar da labarin ba.
Wani da ya halarci taron bikin murnar da Onyeka Onwenu ta yi wasa ya ce,
“Abin bakin ciki ne matuka rasuwar Onyeka Onwenu, ta yi wasa mai ban kayatarwa a bikin zagayowar ranar haihuwar Misis Stella Okoli a yau, bayan ta yi wasan ne ta fadi.
- Isra’ila Ta Halaka Shugaban Hamas Ismail Haniyeh
- An kafa kwamiti Kan Sabon Mafi ƙarancin Albashi A Kano
Onwenu shararriyar marubuciya ce, kuma mawaƙiya, yar jarida, kuma ƴar siyasa, ta yi nasara a harkar waka, an kuma nada ta shugabar majalisar fasaha da al’adu ta jihar Imo.
A shekarar 2013, gwamnatin Goodluck Jonathan ta nada ta a matsayin Babbar Darakta a Cibiyar Kula Da Cigaban Mata ta Kasa (NCWD).
An haifi Onyeka Onwenu ranar 31 ga Janairu, shekarar 1952 kuma ta bar duniya ranar Talata 30 ga Yuli, 2024 a jihar Legas.