Wata sanarwa daga kasar Iran na cewa Isra’ila ta halaka shugaban Kungiyar Hamas Ismail Haniyeh mai shekara 62 a gidansa da ke Tehran.
Sanarwar da Hamas ta fitar yau Laraba da safe ta ce an kashe Haniyeh ne a gidansa da ke Tehran, a ziyarar da yake domin halartar bikin rantsar da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian.
Haniyeh fitacce ne a fafutukar kare haƙƙin Falasɗinawam, ya jima yana gwagwarmaya kan kisan ƙare-dangin da Isra’ila ke yi a Gaza.
- An kafa kwamiti Kan Sabon Mafi ƙarancin Albashi A Kano
- Majalisa Za Ta Yi Zaman Gaggawa Saboda Zanga-zanga
Tuni dai Gwamnatin Iran ta bayyana ƙaddamar da bincike kan kisansan, ta ce tana sa ran fitar da sakamakonsa nan ba da jimawa ba.
Hamas ta ce kisan Ismail Haniyeh babban laifi kuma martanin halaka shi ba zai yi daɗi ba.