• Home  
  • Sheikh Fethullah Gulen Ya Rasu Yana Da Shekaru 83
- Babban Labari - Labarai

Sheikh Fethullah Gulen Ya Rasu Yana Da Shekaru 83

Malamin addini kuma babban ɗan Adawa ga shugaba Racep Tayyib Erdagon a ƙasar Turkiyya Fethullah Gulan ya rasu yana da shekaru 83 bayan rashin lafiya a kasar Amurka

Malamin addini kuma babban ɗan Adawa ga shugaba Racep Tayyib Erdagon a ƙasar Turkiyya Fethullah Gulan ya rasu yana da shekaru 83 bayan rashin lafiya a kasar Amurka.

An an zargi Sheikh Gulan a baya da kitsa juyin mulkin da baiyi nasara ba ga Racep Tayyib Erdagon a shekarar 2016.

Marigayin Malamin ne dai ya samar da ƙungiyar International Islamic Movement kuma na hannun daman shugaba Erdagon kafin a zarge shi da kitsa juyin mulki ga Shugaban.

Sheikh Gulen ya rasu ne a ranar Lahadi a wani asibiti dake ƙasar Amurka, kuma ya yi zaman neman mafaka na sa kai a ƙasar tun shekarar 1999.

Duk da ba’a bayyana musabbabin mutuwar ta sa ba, rahotanni daga makusantansa sun bayyana cewa an kwantar dashi ne asibitin saboda matsalar ciwon ƙoda.

A lokacin da yake jagorantar ƙungiyar siyasa a musulunci a ƙasar, Shugaba Erdagon ya yi amfani da wasu mabiyan sa kuma sun sami muƙamai a gwamnatin sa.

Sai dai a shekarar 2016 ne manyan abokan suka juye zuwa abokan hamayya, inda gwamantin Turkiyya ta ayyana ƙungiyar Sheikh Gulen a matsayin ƙungiyar ta’addanci.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000

Manyan Labarai