Mataimakin Shugaban Najeriya, Sanata Kashim Shettima, ya tashi daga Abuja zuwa Luanda babban birnin Angola, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron shugabannin ƙasashen Tarayyar Afirka (AU) na musamman karo na 21.
Sanarwar da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar ta ce taron zai mayar da hankali kan hanyoyin warware rikice-rikice da kuma bunƙasa zaman lafiya mai ɗorewa a nahiyar Afirka.
Ana sa ran Shettima zai haɗu da sauran shugabannin Afirka domin tattauna kalubalen tsaro da hanyoyin hana tashe-tashen hankula da warware rikice-rikice.
Hakazalika, zai gabatar da jawabin Shugaba Tinubu a taron, inda zai bayyana matsayar Najeriya kan batutuwan da za a tattauna tare da jaddada aniyar ƙasar na ci gaba da tallafa wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin nahiyar.