An murƙushe yunƙurin sojoji na yin bore a Nijar – Gwamnati

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi bayani kan harbe-harben da aka kwashe tsawon dare ana ji har zuwa wayeywar garin Asabar a Yamai, babban birnin kasar inda ta ce ta murƙushe yunƙurin bore da wasu sojoji suka yi.

Lamarin ya tayar da hankulan mazauna birnin tare da jawo hankalin ƙasashen duniya.

A cikin sanarwar da ya karanta ta gidan talabijin na gwamnati, ministan tsaron Nijar, Janar Salifou Modi, ya ce kimanin ƙarfe 12:20 na dare wani rukuni na sojoji sun kutsa cikin sansanin soji na 101 da ke kusa da filin jirgin saman Diori Hamani a Yamai, inda suka yi garkuwa da wasu daga cikin abokan aikinsu.

Sai dai ya ce dakarun ƙasar sun yi gaggawar mayar da martani, inda suka dakile yunƙurin tare da dawo da doka da oda.

“Bayan jajircewar dakarun ƙasar, yanzu komai ya koma daidai kuma an murƙushe boren da suka so tayarwa,” in ji sanarwar gwamnatin.

Kafin wannan bayani daga gwamnati, babu tabbas kan asalin inda ake harbe-harben, kuma ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Ministan bai kuma yi karin haske kan ko akwai wadanda suka rasa rai ko kuma wadanda suka ji rauni ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters dai ya ambato wasu majiyoyin tsaro na cewa an kai hari a filin jirgin saman Yamai tare da yunƙurin kutsawa fadar shugaban ƙasa.

Wasu mazauna Yamai da BBC ta tuntuba sun ce sun ji karar harbe-harbe a kusa da filin jirgin saman Diori Hamani, fadar shugaban ƙasa da kuma wasu sansanonin soji.

Wani mazaunin birnin ya shaida wa BBC cewa: “Tun misalin ƙarfe ɗaya na dare muke jin karar harbe-harbe da kuma wasu abubuwan fashewa.”

Wani mutum na biyu kuma ya ce ya ji karar harbe-harben lokacin da ya tashi sallar asuba.

“Har ma mun yi addu’a a masallaci domin neman wa ƙasar zaman lafiya. Samari sun fito ƙofar gida suna tattaunawa kan abin da ke faruwa. Yawancin mutane na cewa ‘yan ta’adda ne,” in ji shi.

Mazauna birnin sun ce har zuwa wayewar gari ana ci gaba da jin harbe-harbe a wasu sassan Yamai.

Hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna motocin yaƙi masu sulke da aka tura domin ƙarfafa tsaro a yankunan da ke kusa da filin jirgin saman birnin.

Wata majiyar tsaro ta kuma shaida wa Reuters cewa jami’an tsaron Nijar sun yi galaba kan waɗanda suka kai harin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Ta ƙara da cewa wasu daga cikin waɗanda ake zargi sun tsere.

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, inda suka hambarar da gwamnatin da aka zaɓa ta Mohamed Bazoum, Nijar ke fuskantar ƙalubalen tsaro daga ƙungiyoyin mayaƙa masu alaƙa da Al-ƙa’ida da kuma IS.

Ƙasar mai arzikin ma’adanan yureniyom da danyen man fetur ta sauya akalar manufofinta na ƙetare bayan juyin mulkin, inda ta ƙarfafa alaƙa da Rasha tare da nisantar ƙasashen yamma.

Nijar da makwabtan ta Burkina Faso da Mali sun kuma fice daga ƙungiyar Ecowas tare da kafa Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES).

A baya, shugaban ƙasar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya zargi Faransa da hannu wajen ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fuskanta, zargin da Paris ta musant

Post masu alaƙa

Shettima ya tafi Angola domin wakiltar Tinubu a taron AU

‘An koma haƙo man fetur a yankin Kurdistan na Iraq’

Sakataren sojin kasan Amurka zai yi murabus