Ministan Albarkatun Ƙasar Iraq, Kamal Mohammed, ya bayyana cewa an koma haƙo man fetur a yankin Kurdistan bayan hare-haren jiragen sama marasa matuƙa da suka kai wa wasu filayen mai da cibiyoyin samar da shi hari.
Ya ce kamfanonin mai sun koma aiki, kuma yawan man da ake haƙowa a yankin ya kai tsakanin ganga 220,000 zuwa 230,000 a rana.
Ministan ya ce dukkan filayen mai sun koma aiki baya ga filin mai na Sarsang, wanda har yanzu ke fuskantar matsaloli sakamakon barnar da hare-haren jiragen sama marasa matuƙa suka yi masa.
A watan Yulin 2025 ne kamfanin HKN Energy na Amurka, mai kula da filin mai na Sarsang, ya dakatar da aiki bayan wasu hare-hare da suka haddasa fashe-fashe a wurin..