Ana sa ran shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai je birnin landan a yau Laraba, 3 ga watan Mayu, a matsayin amsa gayyatar da masarautar ta Ingila ta yi wa shuwagabannin duniya.
Wannan tabbaci ya fito ne ta bakin Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Femi Adesina, wanda ya kuma bayyana cewa za a yi naɗin ne a ranar Asabar, 6 ga Mayu, 2023.
Sannan kuma, sakataren ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arziƙi Ƙasashen Rainon Ingila, Commonwealth, zai yi amfani da wannan dama wajen gudanar da taron Gamayyar Mambobin Shuwagabannin Ƙasashen da ke wannan Ƙungiyar a ranar Juma’a, 5 ga Mayu, 2023.
Manufar taron dai shi ne tattaunawa kan makomar ƙungiyar da kuma gudunmuwar matasa.
Mutanen da za su yi wa shugaba Buhari rakiya sun haɗa da: Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, da ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama da ministan Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, da Mashawarcin shugaban ƙasan kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno (Rtd), da sauransu.