Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙar rijiyar man fetur a ƙaramar hukumar Obi a jihar Nasarawa da ke Arewa ta tsakiyar ƙasar.
Ƙaddamar da aikin tona rijiyar zai sa kamfanin mai na ƙasar NNPC, ya fara tono man fetur daga jihar.
A cikin watan Nuwamban bara ne dai shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da aikin haƙo man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe a yankin Arewa maso gabashin ƙasar.
Yawancin man da ƙasar ke da shi dai tana haƙoshi ne daga yankin Niger Delta a kudu maso kudancin ƙasar.
Najeriya dai ta dogara ne da man fetur da take fitarwa a matsayin hanayar samun kuɗin shiga,
Duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatocin ƙasar ke yi na faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga ga ƙasar.